18 Satumba 2026 - 14:35
Source: ABNA24
Yemen Tayi Gargaɗin Game Da Faɗaɗa Wuraren Martaninta

Bisa ga wannan batu, faɗaɗa faɗin tsoma baki ko kawo dauki ta waje zai kjai ga faɗaɗa fagagen maida martani. Musamman da yake Yemen ta yi gargaɗin cewa za ta shigar da ƙasashen da ke shiga cikin hadin gwiwa da tallafin soji ga Saudiyya cikin lissafin wadanda zataa fuskantar juna na teku. Wannan al'amari na iya haɗawa da matakan hana wucewar jiragen ruwa ta mashigar Babal-Mandab.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa:, A wani ɓangare kuma, Yemen tana ɗaukar duk wani tsoma baki daga waje ga goyon bayan yaƙin Saudiyya kan Yemen — ko ta hanyar mashawarta da ƙwararru, ko bayanai, ko tsarin kariya ta sama ko tallafin fasaha da kayan aiki — ba tare da la'akari da siffarsa ko girman kasancewarsa a fagen ba, a matsayin shiga ta gaske cikin yaƙi.

Bisa ga wannan batu, faɗaɗa faɗin tsoma baki ko kawo dauki ta waje zai kjai ga faɗaɗa fagagen maida martani. Musamman da yake Yemen ta yi gargaɗin cewa za ta shigar da ƙasashen da ke shiga cikin hadin gwiwa da tallafin soji ga Saudiyya cikin lissafin wadanda zataa fuskantar juna na teku.

Wannan al'amari na iya haɗawa da matakan hana wucewar jiragen ruwa ta mashigar Babal-Mandab.

Bayanan Da Suka Saba Wa Juna Na Isra'ila Game Da Mataki Na Gaba Na Saudiyya

Zaɓuɓɓukan Saudiyya wajen fuskantar nasarorin da ƙungiyar Ansarullah ta samu kwanan nan a Yemen sun ƙara takaita.

A lokacin da Saudiyya ta shiga tattaunawar soji ta yankin da gwamnatin Sahayoniya ma tare da goyon bayan Amurka ke shiga ciki, Riyadh a lokaci guda tana ƙoƙarin samun raguwar tashin hankali ta hanyoyin shiga tsakani.

A cikin wannan tsari, kamfanin dillancin labarai na "Reuters" dangane da wasu jami'an Iran uku ya ba da rahoton cewa Sin ta tuntuɓi Iran a asirce kuma bisa buƙatar Saudiyya daga Tehran ta nemi ta yi amfani da tasirinta don shawo kan ƙungiyar Ansarullah.

Riyadh ta kuma roƙi "Asim Munir" kwamandan sojin Pakistan, da ya tuntuɓi Tehran da wannan manufa ta musamman don hana kai hari kan wuraren tattalin arziki na Saudiyya.

Matsin Lamba Na Lokaci Ɗaya Kan Riyadh

Ana yin waɗannan ƙoƙarin ne a yanayin da matsin lamba kan Saudiyya ya ƙaru.

"Yoel Guzansky" mai bincike na cibiyar nazarin tsaron ƙasa ta gwamnatin Sahayoniya, ya kwatanta waɗannan matsin lamba a matsayin ɗaya daga cikin mafi tsanani cikin shekarun da suka gabata.

A kiyasinsa, Saudiyya tana fuskantar matsin lamba na lokaci ɗaya daga rikicewar zirga-zirga a mashigar Hormuz da kubucewar ikon wannan ƙasar na fitar da ga kuma barazanar ƙungiyoyin Iraki kan ababen more rayuwa na Saudiyya da barazanar Yemeniyawa kan mashigar Babal-Mandab.

Guzansky yayi imani cewa takaitar tallafi daga waje yana takurawa sararin motsi na "Mohammed bin Salman" yariman mai jiran gado na Saudiyya. Musamman bayan da ya yi ƙoƙarin guje wa shiga kai tsaye cikin rikici da kuma buɗe hanyoyin sadarwa da Iran.

A imanin wannan mai bincike, waɗannan matsin lamba na iya tura Riyadh zuwa tattauanwa kai tsaye da Tehran don sake buɗe mashigar Hormuz da amfani da tasirin Iran don dakatar da ƙungiyar Ansarullah ta Yemen da ƙungiyoyin Iraki.

Tabbas ya nanata cewa irin wannan yunkuri bai samo asali daga amincewar Saudiyya ga Iran ba ne, a'a yana da alaƙa da lissafin dakatar da tashin hankali da tabbatar da hanyoyin fitar da kayan masrufi da mai daga kasar Saudiyya.

Guzansky ya kuma yi gargaɗi cewa wannan tsari na iya kai ga nasarorin siyasa ga Tehran kuma ya roƙi Tel Aviv da Washington da su samar wa Riyadh zaɓuɓɓukan aiki a matsayin madadin don kada dogaron Saudiyya kan Iran ya ƙaru.

Taron Sirri Na Shugabannin Soji Na Gwamnatin Sahayoniya Da Ƙasashen Larabawa

Jaridar "Yedioth Ahronoth" ma ta wallafa ƙarin cikakkun bayanai game da wani taron sirri da aka gudanar a Jamus.

An gudanar da wannan taron ne tare da halartar "Eyal Zamir" shugaban hafsan sojin gwamnatin Sahayoniya da takwarorinsa daga ƙasashen Larabawa bakwai waɗanda a cikinsu akwai "Fayyad bin Hamid Al-Ruwaili" shugaban hafsan sojin Saudi Arabiya.

"Brad Cooper" kwamandan hedkwatar rundunar tsakiya ta sojojin Amurka (CENTCOM) ma ya halarci wannan taron.

Dangane da rahoton wannan jaridar, Zamir a cikin wannan taron da aka bayyana manufarsa ƙarfafa dangantakar soji, tsaro da bayanai tsakanin ɓangarorin, ya sanar da mahalarta ayyukan sojin gwamnatin Sahayoniya a Siriya, Lebanon, Zirin Gaza, Yammacin Kogin Jordan da Yemen.

Haɗin Gwiwar Bayanai Da Hanyoyin Madadin Fitar Da Mai

Kamar yadda "Yedioth Ahronoth" ta rubuta, haɗin gwiwar gwamnatin Sahayoniya da Saudiyya tare da shiga tsakani na Amurka a hankali yana samuwa a cikin tsarin shiga cikin bayanai don kare sansanonin soji da ababen more rayuwa na mai.

Wannan haɗin gwiwa ta kuma haɗa da taimako wajen samar da hanyar madadin fitar da mai. Hanyar da za ta iya jigilar mai na Saudiyya zuwa kasuwannin waje ba tare da wucewa ta mashigar Hormuz da Babal-Mandab ba.

"Semadar Perry" marubucin wannan jaridar, ya yi hasashen cewa wannan haɗin gwiwa zai faɗaɗa kuma har ma zai iya kai ga yiwuwar Saudiyya ta shiga wani tsari mai kama da yarjejeniyoyin Abrahim.

…………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha